Bauchi

Bauchi
Wikimedia disambiguation page (en) Fassara
Alamu tanbarin bauchi

Bauchi jaha ce dake yankin Arewacin Najeriya tana yankin Arewacin gabashin Najeriya an kirkiri jihar Bauchi ne a watan Fabrairun shekarar ta 1976 daga tsohuwar jihar Arewa maso Gabas ta gwamnatin Janar Murtala Mohammed. Asali ta hadane da yankin Gombe, wadda ta zama jiha ta daban a shekarar 1996. Tana da kananan hukumomi Ashirin 20. Babban birninta shi ne Bauchi. Jihar Bauchi tana yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, tana da fadin murabba'in kilomita 45,837. Jihar Bauchi tana iyaka da Kano da Jigawa daga arewa sai Yobe da Gombe daga gabas sai jihar Kaduna ta yamma da Filato da Taraba a kudu. Gaba daya yankunan yammacin jihar da arewacin kasar suna da tsaunuka, da duwatsu. Hakan ya faru ne sakamakon kusancin jihar da tsaunukan Jos ta jihar Plateau da kasar Cameroun. Jihar Bauchi na daya daga cikin jahohin Arewacin Najeriya da suka mamaye yankunan ciyayi guda biyu, wato Sudan Savannah da Sahel Savannah. Manyan koguna guda biyu ne suka ratsa jihar, kogin Gongola da Hadejia. Yanayin yanayin jihar Bauchi yana da zafi sosai a watannin Afrilu da Mayu, yayin da Disamba da Janairu ne watanni mafi sanyi. Jihar Bauchi na daya daga cikin jahohin Arewacin Najeriya da suka mamaye yankunan ciyayi guda biyu, wato Sudan Savannah da Sahel Savannah. Manyan koguna guda biyu ne suka ratsa jihar, kogin Gongola da Hadejia. Yanayin yanayin jihar Bauchi yana da zafi sosai a watannin Afrilu da Mayu, yayin da Disamba da Janairu ne watanni mafi sanyi. Jihar Bauchi tana da ƙabilu masu yawa, wanda sun kai ƙabilu 55 da suka haɗa da Fulani, Gerawa, Sayawa, Jarawa, Kirfawa, Turawa Bolewa, Karekare, Kanuri, Fa'awa, Butawa, Warjawa, Zulawa, Boyawa MBadawa. Amma Fulani su ne ƙabila mafi Yewa a Jahar,inda suka mamaye kananun hukumomi irinsu Toro, jama'are, giade, darazo, katagum, misau, Alkaleri, dambam, da dai sauran su. Wannan yana nufin cewa suna da asali,da tsarin sana'a, da sauran abubuwa da yawa waɗanda ke cikin kasancewar al'ummar jihar.


From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Tubidy