Hausawa

Hausawa

Jimlar yawan jama'a
40,000,000
Yankuna masu yawan jama'a
Ivory Coast, Togo, Benin, Burkina Faso, Kameru, Najeriya, Nijar, Sudan, Cadi, Mali, Senegal, Gabon, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Jamhuriyar Kwango, Gini Ikwatoriya, Guinea-Bissau, Gambiya, Ghana, Habasha, Eritrea da Aljeriya
Ginin Hausawa na gargajiya na yumɓu
Shigar Hausawa a ranar Idin Sallah.
Gadon Hausawa na gargajiya.
Rataya, ma'ajiyar Hausawa ce a al'adance.
Shigar Hausawa.
Al adu hausawa
abincin hausawa tuwo DA miyar kuka

Hausa (Sunan mutum ɗaya a jinsin mace da namiji: Bahaushe بَهَوْشٜىٰ‎ (N), Bahaushiya بَهَوْشِيَا‎ (M); Jami'i: Hausawa هَوْسَاوَا‎ da kuma mai gaba ɗaya wato sunan harshen: Hausa;[1] Ajami: مُتَـٰنٜىنْ هَوْسَا‎) al'umma ce dake zaune a arewa maso yammacin tarayyar Nijeriya. Da kudu maso yammacin jamhuriyyar Nijar. Al'umma ce mai ɗimbin yawa, sun bazu a cikin ƙasashen Afirka,[2][3] da kasashen Larabawa, kuma a al'adance masu matuƙar hazaƙa ne, aƙalla akwai fiye da mutane miliyan hamsin waɗanda harshen Hausa shine asalin harshensu. A tarihi ƙabilar Hausawa na tattare a salsalar birane wato alƙarya. Hausawa dai sun sami kafa daularsu ne tun daga shekarun 1300's, sa'adda suka sami nasarori da dauloli kamar su daular Mali, Songhai, Borno, da kuma Fulani, a ƙarni na 19,Hausawa suna amfani da Kuma Doki ne domin yin sufuri da balaguro.[4] Mutane kimanin sama da Kuma miliyan 50, ne ke magana da harshen Hausa a Najeriya da Nijar da Arewacin Ghana da kuma wasu al’umma daga yankin Kaolack a senigal har zuwa khartum dake ƙasar Sudan, Asalin inda zuri'ar Hausawa take shi ne Kano da Katsina da kuma Sokoto.[5] Asalin Hausawa maguzawa ne, amma sun shafe daruruwan shekaru da karɓar addinin musulunci ƙarkashin mulkin sarakunan Haɓe, wanda suka daina yin bori da tsubbace-tsubbace, zuwan Shehu Usman dan Fodio ne yasa ya kawar da mulkin waɗannan sarakunan na ƙasar Hausa, ta hanyar yaƙar Hausawa da sarakunansu na haɓe a Gobir, Zazzau da wasu yankunan ƙasar Hausa. Wanda wannan juyin mulkin ne yasa Shehu Usman ɗan Fodio ya kafa Daular Fulani a Hausa Fulani a ƙasar Hausa, kuma hakan yasa masarautun Ƙasar Hausa sun kasance a ƙungiyar tuta ɗaya ta Usman dan Fodio.[6] Hausawa suna kiran al’adunsu da al’adun gargajiya, wacce suke yi duk shekara, ko a talabijin ko Bidiyo, ko kuma aikace cikin al’amuran yau da kullum.[7] Na daga cikin rubutun Hausawa, suna yin rubutu ne asali da Ajami, rubutu ne da haruffan larabci amman a luggar Hausa, kuma suna rubutawa ne a fallen takarda.[8]

  1. Adamu, Muhammadu Uba (2019). [https://www.worldcat.org/oclc/1120749202 Wane ne Bahaushe? 1. BAHAUSHE Shine wanda mahaifin sa BAHAUSHE ne. 2. Shine wanda ya yarda shi BAHAUSHE ne yana jin farin ciki da daukakar kabilar Hausawa ya kuma yi bakin ciki da nakasunsu sannan kuma baya alaƙanta kansa da ko wacce kabila sai Hausa. Sabon tarihin : asalin hausawa] Check |url= value (help) (Bugu na biyu ed.). Kano: MJB Printers. OCLC 1120749202. line feed character in |url= at position 41 (help)
  2. "Ethnicity in Nigeria". PBS NewsHour (in Turanci). 2007-04-05. Retrieved 2022-12-07.
  3. Godwin, David Leon (2022-04-14). "Top 10 largest tribes in Africa". NewsWireNGR (in Turanci). Retrieved 2022-12-07.
  4. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2008-01-23. Retrieved 2020-12-28.
  5. Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh.p.1
  6. Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh.p.2
  7. Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh.p.11
  8. Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh.p.12

From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Tubidy