Noma

noma
economic sector (en) Fassara da field of work (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na agriculture and forestry (en) Fassara
Bangare na primary sector of the economy (en) Fassara da food system (en) Fassara
Mabiyi gathering (en) Fassara
Lokacin farawa 8 millennium "BCE"
Yana haddasa Gandun daji
Karatun ta Ilimin kimiyyar noma
Tarihin maudu'i history of agriculture (en) Fassara
Uses (en) Fassara arable land (en) Fassara da fresh water (en) Fassara
Classification of Instructional Programs code (en) Fassara 01.0000, 01.00 da 01
NCI Thesaurus ID (en) Fassara C16270
Earliest date (en) Fassara 15 millennium "BCE"
noma Babar Sana,a ne

Hausawa na cewa "Noma na duke tsohon ciniki, noma tushen arziki, kowa ya zo duniya kai ya taras"

  • Menene Noma?
yadda ake huda kenan a lokacin noma
Nuoman shinkafa

Noma yana da kuma ma'anoni da dama kasancewar irin amfaninsa a fannoni daban-daban. To, amma dai a fassara mafi sauki, za mu ce, Noma wata hanyar sana'a ce domin samun abinci da kudin shiga. Haka zalika, noma wata babbar hanya ce ta samun karuwar tattalin arziki da al'ummai suka raja'a a kan ta. A kasar Hausa ko kuwa, noma shi ne babbar hanya ta samun haɓakar tattalin arziki. Da noma ne Hausawa suka fi samun kudin shiga da abinci da ma kayayyakin da ake sarrafawa a masana'anta kamar tufafi da sauransu. A wajen Hausawa musamman mazauna karkara noma ya zama kamar wajibi (dole) a wajen Kuma kowanne Bahaushe, musamman ma magidanci.

Kusan mu ce ma kowanne Bahaushe ya iya noma, ya kuma san yadda ake yin shi. Noma da Kiwo duk suna nufin abu daya ne a ma'anar da ilimin zamani ya samar.


From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Tubidy