Umaru Musa Yar'adua | |||||
---|---|---|---|---|---|
29 Mayu 2007 - 5 Mayu 2010 ← Olusegun Obasanjo - Goodluck Jonathan →
29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007 ← Joseph Akaagerger - Ibrahim Shema → | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Katsina, 16 ga Augusta, 1951 | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Harshen uwa | Fillanci | ||||
Mutuwa | Aso Rock Villa, 5 Mayu 2010 | ||||
Makwanci | Jihar Katsina | ||||
Yanayin mutuwa | (Churg-Strauss syndrome (en) ) | ||||
Ƴan uwa | |||||
Mahaifi | Musa Yar'Adua | ||||
Abokiyar zama | Turai Yar'Adua (1975 - 5 Mayu 2010) | ||||
Ahali | Shehu Musa Yar'Adua | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
Kwalejin Barewa Jami'ar Ahmadu Bello | ||||
Harsuna |
Turanci Fillanci Hausa | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa, university teacher (en) da entrepreneur (en) | ||||
Imani | |||||
Addini | Musulunci | ||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Umaru Musa Yar'aduaYar'adua, ( an haife shi a ranar 16 ga watan Augusta shekara ta alif ɗari tara da hamsin da ɗaya, 1951 – ya rasu a ranar 5 ga watan Mayu shekara ta dubu biyu da goma, 2010) ɗan siyasan Najeriya ne wanda ya kasance shugaban Najeriya daga shekarar dubu biyu da bakwai, 2007 zuwa shekarar dubu biyu da goma, 2010. An ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Najeriya da aka gudanar a ranar 21 ga watan Afrilun shekarar dubu biyu da bakwai, 2007, kuma an rantsar dashi a ranar 29 ga Mayun shekarar dubu biyu da bakwai, 2007.
Ya taɓa zama gwamnan Jihar Katsina daga shekarar alif ɗari tara da chasa'in da tara, 1999 zuwa shekarar dubu biyu da bakwai, 2007; kuma ɗan jam'iyyar PDP ne. A shekarar dubu biyu da tara, 2009, Ƴar'adua ya tafi Saudi Arabia don neman magani na pericarditis. Ya dawo gida Najeriya a ranar 24 ga Fabrairu, shekara ta dubu biyu da goma, 2010, inda ya rasu a ranar 5 ga watan Mayu na wannan shekarar.