Yankin Yamma ta Tsakiya, Najeriya

Yankin Yamma ta Tsakiya, Najeriya

Wuri
Map
 6°19′03″N 5°36′52″E / 6.3175°N 5.6144°E / 6.3175; 5.6144

Babban birni Kazaure
Bayanan tarihi
Mabiyi Western Region (en) Fassara
Ƙirƙira ga Yuni, 1963
Rushewa 27 Mayu 1967

Yankin Tsakiyar-Yamma ya kasance rabon Najeriya daga shekarar 1963, zuwa 1991, daga 1976, ana kiranta da Bendel state.

An kafa shi a watan Yunin 1963, daga Benin da lardunan Delta na Yammacin Yankin, kuma babban birninta shi ne Benin City . An kuma sake canza mata suna zuwa lardi a shekara ta 1966, kuma a shekarar 1967, lokacin da aka raba sauran lardunan zuwa jihohi da yawa, ya ci gaba da kasancewa yanki yanakke, ya zama jiha.

A lokacin yakin basasar Najeriya, sojojin Biafra sun mamaye sabuwar kasar ta Mid-Western, akan hanyarsu ta zuwa Lagos, a kokarin tilasta kawo karshen yakin cikin gaggawa. Yayin da yake karkashin mamayar Biafra, an ayyana jihar a matsayin " Jamhuriyar Benin ". Yayin da sojojin Najeriyar suka sake kwace yankin, jamhuriya ta ruguje ne kwana daya kacal bayan sanarwar lokacin da sojojin Najeriyar suka kame garin Benin.

A shekarar 1976, aka sake yiwa jihar suna Bendel . An raba shi zuwa jihar Delta da Edo a cikin 1991. [1][2]

  1. http://logbaby.com/encyclopedia/history-of-delta-state_10219.html#.UqzIAfTuIQo
  2. "Mid Western Region, Nigeria (1963-1966)".

From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Tubidy